Moniepoint na baiwa kasuwanci damar gudanar da banki ta wayar hannu. Bude asusun kasuwanci, karɓar biyan kuɗi kan layi ko a zahiri, sayen katin waya, biyan kuɗin wuta, tura kuɗi, neman katin kashewa, da samun rancen kasuwanci.
Sama da miliyan biyu na masu kasuwanci sun ba Moniepoint amana don gudanar da asusun bankin kasuwancinsu, suna samun damar cimma burin su na kasuwanci. Moniepoint Business Banking app ya zo domin sauƙaƙa maka hanyoyin gudanar da kuɗin kasuwancinka da samar maka da damammaki marasa iyaka na ci gaba. Mun samar da mafita ta banki mai sauƙi amma ingantacciya ga kowane nau'in kasuwanci da wakilai, yana ba ka damar sarrafa komai daga wayarka ta hannu. Tare da Moniepoint, kasuwancinka zai bunƙasa ba tare da wata tangarɗa ba, yana mai ba ka damar mai da hankali kan abin da ya fi muhimmanci: haɓaka harkokinka.
Samu damar buɗe asusun banki na kasuwancinka cikin mintuna kaɗan, kai tsaye a kan wayarka, da kuma damar aika ko karɓar kuɗi cikin sauƙi ba tare da ɓoyayyun kuɗi ba. Tsare-tsaren ajiyar kuɗi na Moniepoint an tsara su ne don dacewa da buƙatun kasuwancinka, yana taimaka maka adana kuɗi cikin basira. Hakanan, karɓar biyan kuɗi ta katin banki ko transfer ya zama mai sauƙi tare da na'urar POS ta Moniepoint. Kuna iya nema a aiko muku da na'urar POS kai tsaye daga Moniepoint Business Banking app kuma a kawo muku ita cikin awanni 48. Don sarrafa kuɗin fita, katunan kashe kuɗi na Moniepoint zasu taimaka maka wajen bin diddigin yadda ake kashe kuɗi a ainihin lokacin, kuma zaku iya saita iyakokin kashe kuɗi a asusun bankin kasuwancinku. Waɗannan katunan suna da araha kuma ana kawo su gare ku cikin sauri.
Kada ka bari ƙarancin jari ya zama cikas ga ci gaban kasuwancinka. Moniepoint yana ba da rancen jari mai sauƙi ga kasuwanci, tare da ƙaramin ribar kashi 2-3% a wata. Neman rancen yana ɗaukar mintuna biyar kacal kuma zaku sami sanarwar amincewa cikin awanni 48, yana samuwa awa 24 a rana, kwana bakwai a mako. Ban da haka, kowane lokaci da ka sayi kati ko data ta hanyar Moniepoint Business Banking app, zaka sami kashi 2% na kuɗinka a matsayin cashback. A cikin Moniepoint Business Banking app, zaka iya biyan kuɗin bills dinka cikin sauki. Moniepoint Microfinance Bank, wanda Babban Bankin Najeriya (CBN) ke kulawa, ya sadaukar da kansa wajen tallafawa kasuwanci irin naku don su bunƙasa. Zama wani ɓangare na al'ummar Moniepoint na masu kasuwanci sama da miliyan 2 yau!